Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Sakkwato


A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a domin a nasu ganin kamar lamarin ya gagari mahukumta, amma dai suna kara kiraye kirayen samun dauki.

Wannan na zuwa ne lokacin da al'ummomi a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci.

Lokacin azumin Ramadan da hankulan Musulmi suka karkata wajen hidimomin iyali da ibadah, wasu al'ummomi a arewacin Najeriya suna fuskantar matsanancin tashe-tashen hankula ne saboda hadarin da ‘yan bindiga ke jefa rayukansu a ciki.

Wasu al'ummomi a yankin Tureta na jihar Sakkwato, yankin da ke makwabtaka da jihar Zamfara, sun dauki bakuncin ‘yan bindiga wadanda suka abka garuruwansu, suna harbin jama'a tare da satar dabbobi da wasu kayayyaki.

Muryar Amurka ta nemi jin karin bayani daga shugaban karamar hukumar yankin, sai dai bai amsa dukan kiran da aka masa ba.

Duk kiran kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya a Sakkwato shi ma ya ci tura.

Amma mazauna yankin na Tureta sun tabbatar da cewa akwai jami'an tsaro a yankin sai dai yawansu bai wadaci yankunan ba, abinda ya sa matsalar ke ci gaba.

Wani bayani da na samu daga wani jami'in tsaro da baya da iznin magana a hukumance ya tabbatar sun samu rahoton cewa barayi na kan kai hari a garin gidan kare dake bimasa a yankin na tureta.

Wannan lamarin ya na faruwa ne lokacin da Ministan ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammadu Maigari Dingyadi, ke cewa gwamnatin kasar na bai wa sha'anin tsaro kulawar gaske.

Har yanzu dai al'ummomi da dama a yankunan arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin na rashin tsaro tare da jaddada kiraye kiraye ga mahukumta akan samun dauki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
XS
SM
MD
LG