Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Fara Farautar 'Yan Bindigan Da Suka Sace Daruruwan Dalibai A Jihar Neja


Dakarun Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malaman su dake zaune a gidajen ma’aikatan makarantar gwamnati ta kimiya dake garin Kagara a jihar Neja.

Rahotanni da dama sun ce ‘yan bindigan sun fara kai hari a makarantar ne da misalin karfe biyu na daren yau Laraba, inda suka yi ta harbe harbe babu kakkautawa. Ana kyautata zaton wani dalibi ya rasa ransa a cikin harben harben.

Wani jami’I ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, maharan sun shiga makarantar gwamnatin ta Kagaran ce tun cikin dare kana suna yi garkuwa da daruruwar dalibai da malamai.

Ya kara da cewa “daya daga cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa da su da wasu dalibai sun samu damar arcewa. Ma’aikacin ya tabbatar an harbe wani dalibi har lahira a cikin gwagwarmayar sace su,

Makarantar tana da dalibai kimanin dubu daya, amma har yanzu ba a iya gane adadin dalibai da aka yi garkuwa dasu ba. Amma dai ana niyar tattara sauran daliban domin gudanar da lissafi.

Hukumomin tsaro sun yi kokarin gano yadda aka aiwatar da kuma hanyar da aka bi wurin shirya garkuwar, sun kuma fara bin sawun ‘yan biundigan, yayin da jiragen saman soja suka fara shawagi a sararin sama domin gano inda daliban suke.

Satar mutanen na yanzu na zuwa ne kasa da watanni uku da wasu ‘yan bindiga suka sace daruruwan dalibai daga makarantar sakandaren gwamnayi a jihar Katsina. Daga bisani an sako daliban na Katsina bayan tattaunawa fahimtar juna.

Jihohin Neja da Katsina da wasu jihohin arewa maso yammacin da tsakiyar Najeriya na ci gaba da huskantar ayyukan ‘yan bindiga da suke garkuwa da mutane domin samun kudin fansa.

Karin bayani akan: Kagara, jihar Katsina, jihar Neja​, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG