Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sako Yaran Da Aka Sace A Wata Gona


Yaran da aka yi garkuwa dasu
Yaran da aka yi garkuwa dasu

‘Yan sanda sun ce an sako wasu kananan yara 21 da wasu ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata daga wata gona a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Asabar.

Sace-sacen mutane dai ya zama ruwan dare a cikin ‘yan shekarun nan a jihar Katsina yayin da wasu gungun ‘yan bindiga ke sace mutane a makarantu da asibitoci da tituna da gonaki tare da neman kudin fansa daga ‘yan uwansu.

Uku daga cikin iyayen wadanda aka kama sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an sako yaran masu shekaru tsakanin 8 zuwa 14 bayan da iyayen suka biya kudin fansa naira miliyan 1.5 (dala 3,400), amma kakakin rundunar ‘yan sandan Gambo Isa ya musanta cewa an biya kudin fansa.

"An sake su kuma suna tare da iyalansu," in ji Isa a cikin wani sakon WhatsApp da yammacin ranar Asabar.

Iyayen ukun da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters sun nemi a sakaya sunansu saboda fargaban ramuwar gayya daga hukumomi, wadanda ba su amince da biyan kudin fansa ba, ko kuma daga ‘yan fashin da kansu.

“Sun ce idan ba mu biya kudin fansa tsakanin karfe 4 na yammacin ranar Asabar ba za su shiga cikin zurfin dajin tare da su sannan ba za mu sake ganinsu ba,” in ji wani uba.

Ya kara da cewa wasu iyayen sai da suka koma ga ’yan uwa don su taimaka wajen tara kasonsu na kudin.

Iyaye sun ce an yi garkuwa da yara sama da 30 a ranar 30 ga watan Oktoba a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a wata gona da ke tsakanin Kamfanin Mailafiya da Kauyen Kurmin Doka a Katsina, amma wasu sun yi nasarar tserewa.

'Yan sanda da iyayen sun ce duk sauran wadanda aka kama sun samu 'yanci.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG