Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 69 A Jihar Neja


Yan bindiga.
Yan bindiga.

'Yan bindiga sun kashe mutum guda tare da yin garkuwa da 69 a jihar Neja da ke tarayyar Nigeria. Haka kuma mayakan boko haram sun fara kwace mata da karfi a jihar.

Wannan al’amari dai ya faru ne a garin Zazzaga dake yankin karamar hukumar Muya, ya kuma matukar tayar da hankalin mazauna yankin.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa yace maharan sun auka ne a garin na Zazzaga ciki daren wayewar garin Laraban nan dauke da manyan makamai.

Rundunar yan sandan jihar Nejan ta tabbatar da kai wannan hari, sai dai kwamishinan ‘yan sandan, Monday Bala Kuryas ya ce basu da tabbacin adadin mutanen da yan bindigar suka sace.

A halin da ake ciki dai wasu mazauna yankin Shiroro a jihar Nejan da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce mayakan kungiyar boko haram sun fara kwace masu yara mata da karfin tsiya, wai da sunan sun aure su.

Hukumomin jihar Nejan dai sun sha bada tabbacin cewa mayakan na boko haram sun mamaye yankuna da dama a kananan hukumomin Shiroro da Munya, amma suna kokarin fatattakarsu daga wannan yanki mai iyaka da Abuja, fadar gwamnatin Nigeria.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


XS
SM
MD
LG