Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram Sun Kaiwa Sojojin Najeriya Harin Kwantan, Bauna


Sojoji suke sintiri a Kaduna,bayan hargitsin da ya afkawa jihar da wasu sassan arewacin Najeriya.

Da sanyin Asubashin Litinin ne wasu mahara suka kaiwa Sojojin Najeriya harin kwantan bauna a garin Kareto dake karamar hukumar Mobbar a Arewacin Borno. Wanda yake shine yankin da yayi rage a hannun kungiyar Boko Haram.

Jami’an Soja sun fitar da sanarwar da ta tabbatar da cewa tabbas an kaiwa rundunarsu hari a garin na Kareto. A cewar wani Soja da ya tsallake rijiya da baya a harin ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ta wayar Salula cewa suna kokarin gyaran wata motarsu da ta lalace ne maharan suka afka musu, domin alokacin ma basu da isassun kayan aiki a hannunsu.

Maharan dai sun budewa Sojojin wuta wanda cikinsu harda wasu yan kunar bakin wake uku, amma sun sami nasarar dakile ‘yan kunar bakin wake biyu daga cikin maharan, duk da haka dai sojoji da dama sun jikkata sakamakon wannan hari da aka kai.

Sojoji da dama sun rasa rayukansu, haka zalika Sojojin sunyi kokari sosai sun samu sun hallaka maharan da yawa ciki harda yan kunar bakin wake.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG