Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram Sun Sake Abka wa Konduga da Farmaki


‘Yan Boko Haram Sun Sake Abka wa Konduga, Jihar Borno, Fabrairu 12, 2014.
‘Yan Boko Haram Sun Sake Abka wa Konduga, Jihar Borno, Fabrairu 12, 2014.

Mutane da dama sun rasa rayukkansu a cikin hari na biyu da aka kaiwa garin Konduga dake jihar Borno a Nigeria.

Wasu ‘yan bindiga da ake jin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sake kadar wa garin Konduga da hari, inda mutane da dama suka rasa rayukkansu. Izuwa yanzu dai ba cikakken bayani na yawan mutanen da aka hallaka, amma dai an tabattarda an kai harin. Wannan shine hari na biyu cikin kwannaki biyu da aka kai a garin na Konduga dake jihar Borno ta arewa-maso-gabashin Nigeria. A harin da aka kai a ranar Talata akan garin, akalla mutane 39 aka kashe, kuma aka kona daruruwan gidaje, abinda yassa mutanen garin da yawa suka arce, suka bar garin.
XS
SM
MD
LG