Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Democrats dake neman shugabancin Amurka sun yi zazzafar muhawara


Clinton da Sanders lokacin da suke zazzafar muhawara jiya Alhamis
Clinton da Sanders lokacin da suke zazzafar muhawara jiya Alhamis

Masu neman jam’iyar Democrat ta tsayar da su takarar shugaban kasar, dan majalisar dattijai na jihar Vermont Bernie Sanders da tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton sun yi wata zazzafar muhawara jiya alhamis da dare a Brooklyn NY, yayinda ake shirin gudanar da zaben tsaida dan takara a jihar.

Sun yi ta musayar miyau inda suka bayyana tababa kan shawarar da dayan ke yankewa. Sanders wanda a kwanan nan yace bai zaci Clinton ta cancanci zama shugaban kasa ba, ya bayyana jiya cewa, ya amince da tana da kwarewar da zata iya zama shugaban kasa. Sai dai ya bayyana shakku kan shawarwarin da take dauka. Ya yi misali da goyon bayan yakin Iraq da tayi da kuma karbar tallafin kudin yakin neman zabe daga manyan cibiyoyin kasuwancin Wall street.

Clinton ta zargi kanfen din Sanders da yi mata karya. tace al’ummar jihar NY sun zabe ta zuwa majalisar dattijai sau biyu, kuma shugaba Barack Obama ya bata matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka. Tace tana iya yanke hukumcin da ya dace, sai dai ta jadada abinda ta kira raunin Sanders a fannin tsare tsaren kasasahen ketare.

Ta bayyana ci gaba da caccakarta da Sander ke yi kan karbar tallafin kudin kamfen daga manyan cibiyoyin kasuwanci a matsayin sukar da bata da makama.

XS
SM
MD
LG