Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Democrats masu neman tsayawa takarar shugaban kasar Amurka sun fafata jiya


.Sanders da Clinton 'yan Democrats dake neman shugabancin Amurka

‘Yar takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam’iyar Democrat Hillary Clinton da abokin hamayyarta Sanata Bernie Sanders, sun kalubalanci junansu kan batutuwan da suka shafi shigar baki cikin kasar.

‘Yan takarar biyu sun kalubalanci juna ne a wata muhawara da suka tafka a daren jiya Laraba a jihar Florida.

Clinton da Sanders za su fafata a zabukan da za a yi a Florida da kuma wasu juhohi hudu da ke da yawan wakilai a ranar Talata mai zuwa.

Shi dai Sanders ya na so ne ya shammaci Clinton a Michigan domin rufe tazarar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta bashi.

Yayin da suke muhawarar, Clinton ta caccaki Sanders da cewa ya taba kada kuri’ar nuna rashin goyon bayansa kan sauye-sauyen shige da ficen baki a Amurka a shekarar 2007.

Shi kuwa Sanders ya kalubalanci Clinton ne kan kin amincewa da ta yi a bar bakin haure su sami lasisin tuki.

Sai dai dukkaninsu sun ce ba za su amince a mayar da yara da bakin hauren da ba su aikata laifi ba zuwa kasashensu.

XS
SM
MD
LG