Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashin Kan Teku Sun Saki Rashawa Da Dan Poland


Sojojin Jamus tare da dakarun ruwa na Tarayyar Turai, a lokacin da suke kan hanyarsu ta kokarin kama wani jirgin 'yan fashin kan tekun Tanzania. Nowemba 4, 2011.
Sojojin Jamus tare da dakarun ruwa na Tarayyar Turai, a lokacin da suke kan hanyarsu ta kokarin kama wani jirgin 'yan fashin kan tekun Tanzania. Nowemba 4, 2011.

‘Yan kasar Najeriya masu fashin jiragen ruwa sun saki ‘yan kasar Rasha biyar da dan kasar Poland daya da suka sace a watan jiya daga cikin jirgin ruwan su a gabar tekun yankin Najeriya.

WASHINGTON, D.C - Makaniken jirgin ruwan dan kasar Jamus ya tabbatar a yau Talata cewa an saki duka ma’aikatan tun ranar 11 ga watan nan na Mayu, kuma dukan su, su na cikin koshin lafiya kuma har sun koma kasashen su.

Kamfanin bai fada ba ko an biya kudin fansar mutanen, amma yawanci masu jiragen ruwa kan bayar da makudan kudade kafin a saki ma’aikatan su da ake sacewa.

Ranar 25 ga watan Afrilu aka sace ma’aikatan jirgin ruwan, lokacin da ‘yan fashi 14 cikin gagarumar damarar yaki su ka kutsa cikin jirgin ruwa.

Fashin jiragen ruwa na dada karuwa a yankin tekun kudu maso yammacin Afirka, inda akai-akai ‘yan bindiga ke kai hare-hare kan tankokin mai don su saci danye mai kuma su kama ‘yan kasashen waje su yi garkuwa da su sai a basu kudin fansa su sake su.

Hukumar saka idanu kan ruwayen teku ta duniya ta ce a bana ta samu bayanan cewa sau 19 aka yi fashin jiragen ruwa a gabar tekun yankin Najeriya.
XS
SM
MD
LG