Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Kungiyar Boko Haram Sun kai Hari A wasu Sasan Jihar Adamawa


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Alummomin da aka kaiwa harin na boko haram sunce maharan sunzo ne cikin motoci da kuma babura yayin da wasun su akan dawakai inda suka fara diran mikiya a kauyen Gayesa inda suka kashe rayuka a kalla 30 baya da gidajen da suka kona.

Wani ganau ya shaidawa muryar Amurka cewa sunzo da motoci kirar Hilux 4 da dawakai guda 3 da mashuna sun kai 20.

Da aka tambaye ko ba jami'an tsaro ne sai yace jami'an tsaro suna Hong kuma da aka sanar dasu sai suka ce basa aikin dare.

Da kuma aka tambaye shi ko baya ga wannan kauyen na Gayesa sun tafi wani garin ko kauyen anan ko cewa yayi sun tafi wani kauye da ake kira Zang, kuma sun kona garin na Zang gaba dayan sa, sailin nan maharba suka fatattake su suka kore su bada daya,

To sai dai ba a kamala juyayin wannan lamari ba kwaran kuma sai gasu sun sake dawo wa garin na Zang din a kusa da inda suka fara kai harin farko, wanda har sailin rubuta wannan rahoto ba a san halin da ake ciki ba.

Yan kungiyar boko haram - 3'36"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Wannan talikin yaci gaba da bayanin cewa mutane suna ta guduwa domin ko ana ta harbe-harbe , yace har sailin da yake Magana da wakilin wannan gidan radiyon na soja guda da yazo domin kawo dauki.

Hukumomi sun tabbatar da wannan hare-haren na kwanan nan, inda ma gwamnan jihar Barister Bala James Ingilari ta bakin mai Magana da yawun sa PP Elesha ya bukaci wadanda ke kusa da dajin Sambisa da suyi taka tsantsan.

‘’Wadanda ake koro daga wannan dajin suna da makamai wadanda ke hannayen su don haka ayi taka tsantsan, domin duk wanda suka samu zasu yi ramuwar gayya ne akan shi amma bayan kwanaki kadan ko makonni kadan duk makamam dake hannayen su ya kare ba za a sake samun wannan harin ba, amma a yanzu za a yi taka tsantsan don haka wadanda ke wannan wurare a lura da wuri, kuma gwamnati ta riga ta shaidawa jamiaan tsaro abinda yake faruwa, kuma jamiaan tsaro na daukar matakan tsaron da suka cancanta domin kawo karshen wannan al’amari”

Wannan hare-haren dai yana zuwa ne yan awoyi kadan da wasu jiragen sama suka watso wasu takadun dake bayanin cewa mayakan book haram suna nadama akan abin da suka aikata yayin da gefe guda kuwa hedikwatan tsaron kasar ke bayyana irin nasarorin da suke cewa suna samu kan mayakan book haram, batun da masana harkokin tsaro irin su Muhammad Abdulhamid da Dr Bawa Abdullahi Wase kewa karatun ta natsu

XS
SM
MD
LG