Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kwana-kwana Na Cigaba Da Dauki Ba Dadi Da Wutar Daji A Jihar California


A jahar California, 'yan kwana-kwana na can suna kokarin kashe wutar daji daban daban fiye da 12, tuni gobarar dajin suka hallaka akalla mutane 10, suka tilastawa dubban mutane gudu daga gidajensu.

Jami'an hukumomin kashe gobara a jiya Litinin suka yi kiyasin cewa zuwa yanzu gobarar dajin daban daban sun kona gidaje da wuraren kasuwanci 1,500, yayin da asibitoci suka ce fiye da mutane 100 ne suka nemi jinya sakamkon shakar hayaki.

Ana kyautata zaton adadin wadanda wutar dajin ta halaka zai karu.

Har yanzu dai ba'a san musabbabin wutar dajin da suke ci a sassan jahar da dama ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG