Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Matan Dapchi Sun Koma Gida


Lokacin da ake jigilar 'yan matan Dapchi daga Abuja zuwa Maiduguri
Lokacin da ake jigilar 'yan matan Dapchi daga Abuja zuwa Maiduguri

Rahotanni daga Najeriya na cewa daliban makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace ta kuma sako su, sun koma gida bayan da aka kai su Abuja, babban birnin Najeriya.

A yau ne daliban sakandaren Dapchi suka bar Abuja, inda wani jirgin sojojin sama na Najeriya samfurin C30 Haculean ya yi jigilarsu zuwa Maiduguri, a jihar Borno.

Daga nan kuma za a debe su zuwa garin Dapchi da ke jihar Yobe bisa rakiyar mayakan sama, kamar yadda wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina ya tabbatar.

Kakakin hedkwatar rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya cikin sanarwar da ya aikewa Sashin Hausa na Muryar Amurkan, ya ce babu wata matsala da aka fuskanta wajen wannan hidima.

A makon da ya gabata ne mayakan Boko Haram suka maido da ‘yan matan su 106 da wani yaro namiji daya.

Daga nan ne kuma aka garzaya da su Abuja, babban Birnin Najeriya inda har suka gana da shugaba Muhammadu Buhari.

An sace ‘yan matan ne su 110 a ranar 19 ga watan Fabrairu a makarantar kwaleji ta gwamnati da ke Dapchi.

Amma 105 ne suka samu kubuta yayin da wasu biyar suka halaka, kana wata daliba daya da ake kira Leah Sharibu, ke ci gaba da zama a hannun mayakan.

Rahotanni sun ce an ki sakin Leah ne saboda ita Kirista ce, lamarin da ya janyo suka daga sassan Najeriya, ciki har da na kungiyoyi addinin Islama.

Amma shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, a jiya Asabar ya ba da tababcin cewa Leah na gab da komawa gida.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG