Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya 379,000 Su Ka Nemi Aiki A Gurabu 4,000 Na Hukumar Shige Da Fice.


ABUJA: Muhammadu Babandede Nigerian Immigration Control General.
ABUJA: Muhammadu Babandede Nigerian Immigration Control General.

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta bayyana cewa adadin mutane 379,000 ne suka nemi aiki, a gurabu aiki 4,120 da ta ayyana tana bukatar daukar ma'aikata domin cike su.

Babban kwanturolan hukumar ta shige da fice ta kasa, Mal. Muhammad Babandede ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce a ciki adadin mutanen da suka nemi aikin, mutane dubu 6,145 ne hukumar ta gayyata don samun horo.

Hukumar ta dauki mutane daga dukan kananan hukumomin Najeriya daga cikin wadanda suka samu nasarar gayyatar da ta yi, kuma ta gayyaci kimanin kaso goma-goma a dukan jihohin kasar bisa la’akari da cancanta da amfani da tsarin raba-daidai na daukar aiki a bisa kundin tsarin mulkin kasar.

Babandede ya kara da cewa, duk jami’in da ya sami nasarar samun aikin dole ne a yi masa gwajin tu’amali da miyagun kwayoyi, haka kuma duk wanda aka gano alamar tu’amalli da miyagun kwayoyin ba zai samu damar aikin ba.

Haka kuma, Babandede ya ce, har yanzu hukumar na kan matsayinta game da wa’adin da ta sanya na matakin samar da fasfo ga wadanda suka neman tun watannin baya amma aka sami tsaiko, ya ci gaba da cewa kuma a halin yanzu akwai fasfo dubu 23,907 da masu nema ba su zo sun karba ba.

Babban kwanturolan hukumar ya ce yankin Ikoyi na jihar Legas ne ke da mafi yawa na adadin mutanen da ba su karbi fasfo din su ba, da adadinsu ya kai sama da 7,000.

Yace hukumar a shirye ta ke ta samar da adadin fasfo 130,000 zuwa 150,000, daga ranar Alhami zuwa ranar 31 da ga watan Mayun da muke bankwana da shi, a yayin da za a samar da dubu 58 a cikin gida don cika alkawarin wa’adin da ta sanya, in ji Babandede.

A halin yanzu dai, ba bu wani hukunci kan duk wanda bai karbi fasfo din sa ba kafin wa’adin ranar 31 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG