Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Su Na Nuna Fusatarsu Da Janye Tallafin Farashin Mai


Masu zanga-zangar nuna kin jinin janye tallafin farashin man fetur a Lagos, talata 3 Janairu, 2012.
Masu zanga-zangar nuna kin jinin janye tallafin farashin man fetur a Lagos, talata 3 Janairu, 2012.

'Yan zanga-zanga sun yi maci a Lagos dauke da kwalaye su na yin tur da shugaba Goodluck Jonathan da kuma matakin janye tallafin farashin

'Yan zanga-zanga sun yi maci a Najeriya domin nuna rashin jin dadin matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kawo karshen tallafin farashin man fetur, matakin da ya sa farashin yayi tashin gwauron zabi cikin kwana guda a wannan kasa mai arzikin man fetur.

A yau masu zanga-zanga a Lagos suka ratsa birnin dauke da kwalaye na sukar lamirin shugaba Goodluck Jonathan. Wasu daga cikin 'yan zanga-zangar sun bi ta gidajen mai inda suka hana aiki a wuraren.

Amma kuma jami'an gwamnatin Najeriya su na ci gaba da bayyana irin alherin dake tattare da janye wannan tallafin farashin wanda yake lashe ma kasar kudi har dala miliyan dubu 7 da dari biyar a kowace shekara.

Ministar albarkatun man fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, ta fada yau talata cewa al'ummar Najeriya da kuma tattalin arzikin kasar za su ga amfanin wannan janyewa nan take.

Shugaba Jonathan yace kawo karshen tallafin farashin zai ba gwamnati sukunin samun kudaden samar da kayan bukatu tare da aiwatar da shirye-shiryen kyautata jin dadin jama'a.

Tallafin farashin man fetur na daya daga cikin abubuwa kalilan da talakan Najeriya ke cin moriyarsu daga arzikin man fetur na kasar. Akasarin talakan Najeriya ba ya samun abinda ya shige Dala 2 a rana, kimanin Naira 300.

Manyan kungiyoyin kwadagon kasar, NLC da TUC, sun ce janye tallafin farashin man fetur din "rashin imani da rashin tunani" ne.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG