Accessibility links

Kungiyoyin Kwadago Sun Lashi Takobin Ci Gaba Da Yajin Aiki


'Ya'yan kungiyar lauyoyi ta Najeriya cikin jerin wadanda suka yi zanga-zanga litinin a Lagos domin nuna fusata da janye tallafin farashin man fetur.

A rana ta biyu da fara tayar da kayar baya, matasa a fusace sun toshe hanyar shiga wata unguwar masu hannu da shuni a Lagos

Kungiyoyin kwadago a fadin Najeriya sun lashi takobin ci gaba da yajin aiki tare da tayar da kayar baya a fadin kasar a rana ta biyu a yau talata, domin nuna rashin yardarsu da farashin man fetur da ya cira sama a makon da ya shige, a bayan da haka kwatsam gwamnati ta janye tallafin farashin man fetur.

A yayin da aka shiga rana ta biyu da wannan yajin aikin, matasa a fusace sun baza tayoyi suka cunna musu wuta, suka tare hanyar shiga wata unguwar masu hannu da shuni a birnin Lagos, cibiyar harkokin kasuwanci ta kasar.

Wasu 'yan zanga-zangar dauek da duwatsu, sun yi ta sukar lamirin gwamnati, inda har aka ji wani mai suna Danjuma Mohammed na cewa, "Ba mu tsoronku a yanzu, idan yaki kuke nema mun shirya."

ba a dai samu rahoton tashin hankali ba a yau talata, koda yake motoci kalilan ke zirga-zirga a kan manyan hanyoyin motar kasar, kuma akasarin kantuna da kamfanoni su na rufe.

An kashe mutane akalla uku a arangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a jiya litinin, yayin da dubban mutane suka bazu kan titunan kasar domin matsa lamba kan gwamnati da ta maido da tallafin farashin man fetur din.

Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta ki yarda ta maido da tallafin farashin man, tana mai fadin cewa gwamnati ba ta da kudin da zata iya yin hakan. yace kawar da tallafin zai sa gwamnati ta yi tsimin akalla dala miliyan dubu 8 a wannan shekara, kudin da yayi alkawarin za a yi amfani da shi wajen ayyukan kyautata jin dadin jama'a da samar da kayayyakin bukatu.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG