Accessibility links

'Yan Najeriya Sun Yi Addu'oin Tunawa Da Solomon Lar a Amurka

  • Grace Alheri Abdu

Solomon Lar

Yan Najeriya mazauna Amurka sun yi wani taron addu’o domin tunawa da rayuwar Chief Solomon Lar da ya rasu ranar Laraba a wani asibiti dake nan Amurka

An bayyana marigayi Chief Solomon Daushep Lar a matsayin mutum mai kishin kasa da kaunar zaman lafiya.

Jakaden Najeriya a Amurka farfesa Adebowale Ibidapo Adefuye wanda ya wakilci shugaban kasar Goodluck Jonathan a wajen wani taron adduo’i da aka shirya domin karrama Cif Solomon Lar, ya yaba hangen nesa da halin dattako na marigayin.

Prof Adefuye ya bayyana irin gwaggwarmaya da fafatukar da marigayin ya yi dukan rayuwarshi na ganin an sami zaman lafiya da fahimtar juna a kasar. Ya kuma yaba rawar da Cif Solomon Lar ya taka a kokarin dinke baraka tsakanin bangarorin jam’iyar PDP mai mulki a Najeriya.

Shima a nashi jawabin, jakaden Najeriya a kasar Canada farfesa Ojo Maduake wanda ya wakilci shugaban jam’iyar PDP na kasa Bamanga Tukur, ya bayyana marigayin a matsayin uba wanda yake rungumar kowa ba tare da kula da banbancin addini ko kabila ba.

Farfesa Maduake ya bayyana rawar da Cif Lar ya taka a kafa jam’iyar PDP da kuma renonta zuwa matakin da take a halin yanzu.

A nata jawabin maidakin marigayin Ambasada Prof Mary Lar, tace wasiyar da marigayin ya bari ‘yan mintoci kafin rasuwarshi, ita ce bukatar ganin Najeriya, da Jam’iyar PDP da jihar Plateau da al’ummar Tarok da kuma iyalinshi sun hada kai sun kuma ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya.

Shima a nashi jawabin, shugaban kungiyar ‘yan jihar Plateau mazauna Amurka Hubert Sheldas ya bayyana marigayi Cif Sololon Lar a matsayin mai tsoron Allah da kuma burin ganin matasa sun sami kyakkyawan fandeshan.

Taron da kungiyar ‘yan asalin jihar Plateau ta shirya tare da hadin guiwar kungiyar ‘yan arewacin Najeriya mazauna Amurka da ofishin jakadancin Najeriya a nan Amurka, wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Najeriya dake Washington, DC, ya sami halartar jama’a daga dukan bangarorin Najeriya da kuma ‘yan’uwa da abokai daga kasashe dabam dabam.

Marigayi Solomon Daushep Lar wanda kafin ya shiga siyasa tsohon lauya ne, ya yi aiki a fannoni dabam dabam. Ya zama gwamnan farin kaya na farko a jihar Plateau, ya kuma kasance daya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyar PDP ya kuma zama shugaban jam’iyar na farko. Chief Solomon Lar ya yi aiki a matsayin ministan harkokin ‘yan sanda. Ya kuma yi aiki a kwamitocin sasanta kasa da dama. Kafin rasuwarshi, marigayi Lar yayi kokarin dinke barakar da aka samu a jam’iyar PDP mai mulkin Najeriya.

Chief Solomon Lar ya rasu ranar Laraba a wani asibiti dake nan Amurka bayan doguwar jinya.

Ya rasu ya bar matarshi da ‘ya’ya uku da suka hada da Beni Lar shugabar kwamitin kare hakin bil’adama a majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya.
XS
SM
MD
LG