Accessibility links

Yan sanda sun kashe wani da yake yunkurin kai harin bom a sakatiryar rundunar


Wani jami'in dan sanda a Najeriya.

Yan sanda a arewacin Najeriya sun ce sun harbe suka kashe wani mutum da yake kokarin shiga sakatariya ta ‘yan sanda da mota da aka nasawa bam.

‘Yan sanda a arewacin Najeriya sun ce sun harbe suka kashe wani mutum da yake kokarin shiga sakatariya ta ‘yan sanda da mota da aka nasawa bam.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno Simeon Midenda yace jami’an tsaro a shelkwatar ‘yan sandan ne suka kashe mutumin jiya litinin, lokacin da yayi kokarin kutsawa da mota cikin harabarsu dake birnin Maiduguri yayin da ake tantance wadanda suka je domin shiga aikin ‘Yan sanda.

Yace motar an dankare motar da mutumin yake tukawa da cilindojin hodar gas da kuma man fetur.

‘Yan sanda suna aza laifin harin kan kungiyar Boko Haram, wata kungiyar tsagera masu da’awar Islama, wadanda ake azawa alhakin jerin hare haren boma bomai da kashe kashe a Maiduguri. Galibin hare haren ana auna su ne kan ‘yan sanda da kuma jami’an gwamnati.

Har yanzu dai a arewacin Najeriya, an kashe akalla mutane 10 a wata arangama a birnin Jos. Rahotanni sunce an gwabza fadan ne da jami’an soja.

XS
SM
MD
LG