Accessibility links

Wakilan Dan Kwallon Kafa John Obi Mikel, Sun Ce Ya Sami Sakon Nemar Kudin Fansar Sakin Ubansa

  • Ibrahim Garba

Dan kwallo John Obi Mikel da sauran takwarorinsa.

Wakilan shahararren dan kwallo dan asalin Nijeriya din nan wato John

Wakilan shahararren dan kwallo dan asalin Nijeriya din nan wato John Obi Mikel, sun ce ya sami sakon nemar kudin fansa kafin a saki mahaifinsa.

An kasa gano Michael Obi tun ranar Jumma’ar da ta gabata a birnin Jos da ke yankin tsakiyar kasar, kuma wani danginsa y ace garkuwa aka yi das hi.

Wata kafar nishadantarwa ta wasannin motsa jiki t ace rahoton bukatar kudin fansa $130,000 kafin sakin uban Mikel din ba gaskiya ba ne.

To amman rahotan wani rahoton ya nuna cewa masu garkuwa sun bukaci makudan kudaden fansa, kuma har ma an fara tattaunawa kan yadda za a saki uban cikin koshin lafiya.

John Mikel Obi na wa kulob din Chelsea wasa ne a gasar Premier ta Ingila. Wani bayani daga kamfanin yada labaran SEM y ace Mikel na niyyar buga kwallo wa Chelsea a karshen wannan makon bayan samin karfin gwiwar day a yi daga danginsa.

‘Yan Sandan Nijeriya dai sun bayar da cikiyar uban Mikel, kuma sun sanar jiya Laraba cewa sun sami motar uban. To amman ‘yan sanda bas u bayar da cikakken bayani ba.

XS
SM
MD
LG