Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da 'Yan Siyasar Nijar Ke Cewa Kan Juyin Mulkin Da Aka Yi


Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer
Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer

Bangarorin siyasa a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da wasu sojoji suka ba da sanarwar kifar da shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, yayin da jam’iyar PNDS mai mulki ke cewa za ta yi gwagwarmaya don mayar da hambararen shugaban akan kujerarsa.

NAIMEY, NIGER - ‘Yan adawa a kasar na kallon matakin sojojin a matsayin wani abin ishara ga shugabannin kasashen Afrika.

A titunan Yamai babban birnin kasar al’amura sun fara dawowa kamar yadda aka saba inda jama’a ke ci gaba da harakokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

Da yake magana a madadin uwar jam’iyar PNDS Tarayya da hantsi, kakakinta na kasa, Iro Sani, ya bayyana cewa babu wata hujjar hambarar da gwamnatin ta shugaba Mohamed Bazoum a bisa la’akari da manyan ayyukan da ta sa gaba da nufin inganta rayuwar ‘yan kasa.

Jam’iyyun adawa a nasu bangare sun kira taron gaggawa a cibiyar jam’iyyar Moden Lumana domin nazari akan wannan al’amarI.

A wata sanarwar da suka bayar ba da dadewa ba sojojin kwamitin CNSP sun ce sun dakatar da ayyukan jam’iyun siyasa sannan sun bayyana rashin jin dadinsu bayan da wani jirgin Faransa ya sauka da sanyin safiyar Alhamis a filin jirgin saman Diori Hamani.

Sojojin sun yi wa Faransar kashedi kan ta mutunta matakin rufe iyakokin kasar da aka dauka a sakamakon wannan juyin mulki.

Wasu majiyoyi sun ce sojojin na tattaunawa domin tantance wanda zai shugabanci kwamitin na CNSP yayin da tawagar jami’an kungiyar CEDEAO ko ECOWAS ke kokarin ganawa da bangarorin.

A daya bangare daruruwan magoya bayan wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi gangamin a dandalin Palce de La Concertation don ba da goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Abin Da 'Yan Siyasar Nijar Ke Cewa Kan Juyin Mulkin Da Aka Yi.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG