Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Kashe Fararen Hula 37 A Kauyen Darey Dey Jihar Tilabery


‘Yan bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

Lokacin jana’izar wasu da ‘yan bindiga suka kashe.

‘Yan ta’adda na ci gaba da karkashe fararen hula a yankin Tilabery na jamhuriyar Nijer inda ko a jiya litinin ma wasu gwamman fararen hula akasarinsu mata da yara kanana suka gamu da ajalinsu sakamakon harin da ya rutsa da su a kauyen Darey Dey na gundumar Banibangou.

Sai dai kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani akan wannan sabon hari ba.

Wannan mummunan al’amari ya faru ne a jiya litinin da rana lokacin da ‘yan bindiga suka zo akan babura suka bude wuta kan manoma a dai dai lokacin da suke halartar wani aikin gayya abinda ya yi sanadin mutuwar mutane 37 cikinsu har da yara 14 da mata 4 yayinda wasu mata 4 suka ji rauni kamar yadda wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba ya bayyana mana.

Yace jiya a wajejen karfe 2 da minti 47 na rana wasu ‘yan bindiga suka zo akan babura kimanin 21 kowane babur na dauke da mutane 2 wadanda suka iske mutane a gona suka bude masu wuta.

Ya kara da cewa, "Mu dai mutanen Darey Dey ba mu san abinda ya hada mu da ‘yan ta’adda ba suna yi mana kisan dauki dai-dai kuma mun yi ta kai kukanmu wajen hukumomi amma har yanzu ba a dauki mataki ba a wannan yanki namu soja ko 1 ba mu gani ba wanda zai kare rayukanmu. Tun karfe 2 na ranar jiya litinin ne abin nan ya faru amma sai a karfe 7 na safiyar yau ne jami’an tsaro suka zo mana. Matan nan 4 da suka ji rauni, nan suka wuni suka kwana yashe."

Malan Ganda Saley shugaban kungiyoyin kare hakkin yara CONAFE Niger, ya bayyana cewa, kisan fararen hula wani abu ne da ake ganin ‘yan bindigar yankin sahel na neman mayar da shi sabon salon yaki.

Fararen hula kusan 90 ne aka kiyasta cewa ‘yan ta’adda sun kashe a karkarar Darey Dey ta gundumar Banibangoun jihar Tilabery daga watan maris din da ya gabata kawo yau galibinsu a gonaki ko kuma akan hanyar zuwa gona lamarin da ke barazana ga ayyukan noma a yankin da matsalar tsaro ta durkusar da komai na harkokin tattalin arziki. a makon jiya wani rahoton kungiyar HRW ya gargadi hukumomin Nijer akan bukatar daukan matakan baiwa jama’a kariya a jihohin Tahoua da Tilabery masu makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso inda ‘yan ta’adda suka kashe mutane kimanin 420 a watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2021.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG