Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 100 Ne 'Yan Ta'adda Suka Kashe a Yankin Tillaberi Na Nijer


Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijer
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijer

Mutane fiye da 100 ne aka kashe a jamhuriyar Nijar, a lokacin zaben shugaban kasar, a wasu hare-hare da aka kai kauyuka biyu, wannan shine kisan gilla mafi muni da aka yi a kan fararen hula a kasar, da ma kasashen yankin hamada da ke fama da ‘yan ta’adda.

“Yanzu muka dawo daga inda aka kai harin, wanda aka kai a ranar Asabar.” A kauyen Tchoma Bangou an kashe kusan mutum 70, sai kauyen Zaroumadareve inda aka kashe mutum 30, a cewar Almou Hassane, shugaban karamar hukumar Tondikiwindi, wanda kauyukan biyu suke karkashin shugabancin shi.

Ya kuma kara da cewar. “Akwai kuma wasu mutum 25 da suka samu raunuka, an garzaya da wasunsu birnin Yamai, wasu kuwa zuwa Ouallam don samun magani.”

Sai dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin na ranar Asabar da aka kai a kan babura.

Almou, ya ce ‘yan ta’addan sun rabu gida biyu, inda kashi daya suka kai hari kauyen Zaroumadareye, wasu kuma suka kai a kauyen Tchoma Bangou, kauyukan dai na da tazarar kilomta 7 a tsakaninsu.

Kauyukan biyu masu nisan kilomita 120 daga arewacin babban birnin kasar Yamai, suna cikin yankin Tillaberi ne mai iyaka da Mali da kuma Burkina Faso. A cikin shekaru da dama, kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi suna yawan auna wannan yanki da ake kira “mai iyakoki uku.”

Wata tawagar gwamnati karkashin jagorancin Firaminista Brigi Rafini ta kai ziyara a wurin, yayin da shima shugaban kasa mai barin gado Mahamadou Issoufou zai jagoranci hukumar tsaron kasa da wannan safiyar Litinin.

Shugaba Issoufou ya aike da sakon jaje ta shafinsa na twitter ga al’ummar Tchoma Bangou da Zaroumadareye biyo bayan harin na rashin imani da ‘yan ta’addar suka kai a wadannan kauyuka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG