Accessibility links

'Yansanda Sun Kashe Wani Dake Haramar Kunar Bakin Wake A Maiduguri

  • Aliyu Imam

Wani gandurova yake wucewa kusa da wata mota da ta kone a wani rikici a Bauchi.

‘Yansanda a arewcin Najeriya sun ce sun harbe suka kashe wani mutum da yake kokarin shiga sakatariyat ta ‘yansanda da mota da aka nasawa bam.

‘Yansanda a arewcin Najeriya sun ce sun harbe suka kashe wani mutum da yake kokarin shiga sakatariyat ta ‘yansanda da mota da aka nasawa bam.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Borno Simeon Midenda yace masu aikin tsaro a helkwatar ‘yansandan ne suka kashe mutumin jiya litinin, lokacinda yayi kokarin kutsa kai cikin harabarsu dake binrin Maiduguri yayind ake tanatance mutane da suka zo domin shiga aikin ‘Yansanda.

Yace motar da mutumin yake tukawa an dankara ta da cilindojin fodar gas d a kuma man fetur.

Yansanda suna aza laifin harin kan kungiyar Boko Haram, wata kungiyar tsagera masu da’awar Islama,wadanda ake azawa alhakin jerin hare haren boma bomai da kashe kashe a Maiduguri. Galibin hare hare nana auna su ne kan ‘yansanda da kuma jami’an gwamnati.

Har yanzu dai a arewacin Najeriya, an kashe akalla mutane 10 a wata arangama a birnin Jos. Rahotanni sunce an gwabza fadan ne da jami’an soja.

XS
SM
MD
LG