Accessibility links

'Yansanda Sun Mamaye Ofishin Sabuwar PDP A Fatakwal


Hira da Shugaban Jam'iyyar PDP na Nigeria kan tsarin Karba-Karba

Gap da 'yan sabuwar jam'iyyar PDP suka kaddamar da bude ofishinsu da kafa tutoci sai 'yansanda suka yi masa dirar mikiya.

An bude ofishin sabuwar jam'iyyar PDP a birnin Fatakwal to amma tafiya bata yi nisa ba sai 'yansanda dauke da makamai suka yiwa wurin tsinke inda aka yi dauki ba dadi.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Rivers Chief Tony Okocha shi ne ya yi jawabi a wurin bikin bude ofishin inda ya lissafa jihohin da suke bayan sabuwar PDP din wadanda suka hada da jihar Rivers. Bayan sun kafa tutoci sai daruruwan jami'an tsaro dauke da makamai suka kewaye ofishin inda aka yi taho mu gama. 'Yansandan sun fatartaki mutane suka kuma cire tutocin.

Wasu sun fadi albarkacin bakinsu inda suka ce 'yansiysa tamkar suna rawa tsirara ne a bainar jama'a. Sun ce mutanen Najeriya sun sadakar da rayukansu da dukiyoyinsu domin samun dimokradiya amma sai gashi 'yan siyasa sun sa abubuwa sun tabarbare. Wani Alhaji Musa Saidu dan jam'iyyar PDP ya ce tun lokacin Obasanjo munafikan dake cikin jam'iyyar suke ta tada hankalin mutane. To yanzu sun fito sun dagula harkokin jam'iyyar.

Lamido Abubakar Sokoto nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG