Accessibility links

Har Yanzu Tsugune Bata Kare Ma Jam'iyyar PDP Ba


Hira da Shugaban Jam'iyyar PDP na Nigeria kan tsarin Karba-Karba

Bisa ga duk alamu tsugune bata kare ma jam'iyyar PDP ba wadda ta shiga wani munmmuan rikicin siyasar cikin gida da ya kai ga rabuwarta gida biyu.

Da alamun babu sauki a rikincin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar dake mulki a Najeriya inda gwamnonin da suka balle suka ce sai sun ga abu da ya tube wa buzu nadi.

Wannan lamarin na zuwa ne yayin da masu fashin baki ke tofa albarkacin bakinsu game da harkokin siyasa a kasar. Kwamred Abdullahi Janaral na kungiyar tabbatar da adalci a kasar ya ce zai ba 'yan siyasar arewa shawara cewa kada su bari a yaudaresu kana a yi anfani da su. Ya ce a zububukan da suka wuce an yi anfani da sarakuna da malaman addini kana aka jefa kasar cikin halin da take ciki yanzu. Ya ce yanzu ya kamata mutane su farga.

Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako dake cikin gwamnoni kabwai da suka balle da kuma suka ki karbar gayyatar liyafar cin abinci da shugaban kasa ya shiryawa 'yan jam'iyyarsu a karshen mako ya ce sun shirya tsaf su kalubali duk wani abu da ka iya tunkararsu. Ya ce idan sun turo masu karnukan farauta zasu zo su samu kura. Ya ce idan an ce a yi adalci wannan laifi ne. Ya ce yaya wadanda ke bata PDP za'a barsu su cigaba. Shi kuma Alhaji Baba Suleiman Jada cewa ya yi matakin rufe sakatariar sabuwar PDP da karfin soji bai dace ba. Ya ce ba siyasa ba ce a ce za'a farma wadanda suka balle kamar yadda Bamanga Tukur ya ce zasu yiwa 'yan tawaye. Ya ce idan da Bamanga Tukur shi ne shugaban kasa da ya kashe mutane. Ya ce idan wadanda suka balle suna yi ne don gaskiya kuma tsakinsu da Allah to za'a samu warware matsalar kasar.

Sai dai wasu daga bangaren Bamanga Tunkur sun ce 'yan tawayen suna yin hakan ne domin cimma tasu manufar. Hindu Livinus wani magoyin bayan Bamanga Tukur ya ce tun da siyasar son kai ce to su dan yi hakuri. Ya ce kamar sun mayarda abun wata takardama tsakanin kudu da arewa. Yakamata su tsaya su natsu su sake duba lamarin.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG