Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Philippines Sun Kashe Wani Magajin Gari da Zargin Yana Safarar Miyagun Kwayoyi


Wurin da 'yansanda suka kashe Samsudin Dimaukon

Yan sanda sun harbe wani magajin gari a kasar Philippines da Shugaban kasar Rodrigo Duterte ya bayyana a fili cewa yana da alaka da haramtacciyar hanyar sai da miyagun kwayoyi.

Magajin garin ya gamu da ajalinsa ne a wani fafatawa da bindigogi da suka yi da jami’an tsaro yau Jumma’a.

Magajin Garin Datu Saui Ampatuan Samsudin Dimaukon tare da wasu mutane tara dukansu dauke da bindigogi ne yansandan suka kashe a fafatawar da sukayi dasu.

Kafofin yada labarai sun ce mutanen da suke biye da Magajin garin ne suka fara harbin yansanda a wani shingen bincike da aka saka a hanya a garin Makilala dake Arewacin Yankin Cotabato.

Shugaban yansanda na yankin Sufrtanda Romeo Galgo karami y ace, “ Wannan yaki da miyagun kwayoyi ne na hakika, amma mutanen suka fara harbin mu”.

Duterte yaci zaben shugabancin kasa a farkon wannan shekarar da yawa saboda alkawarin aiwatar da zazzafan yaki da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma bata gari.

Yansandan Philippines da kuma yan kato da gora sun kashe kusan mutane 3,600 akan amfani da Kwayoyi ko kuma sayar dasu tun daga lokacin da Duterte ya karbi ragamar mulkin kasar a watan Yuni.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG