Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yar Shekara 14 Ta Ki Amincewa Da Auren Wuri Don Burin Zama Likita


Asma'u Dauda
Asma'u Dauda

A Najeriya dai gwamnatoci da wasu hukumomi na duniya sun dade suna fafutuka kan habaka sha'anin ilimin ‘ya'ya mata da rage auren wuri ga ‘yan mata, kuma fafutukar na ci gaba da samun karbuwa a wasu jihohin kasar.

Makarantar Malam Sa'idu Taka Tuku da ke jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya, daya ce daga cikin makarantun allo da ake hada ilimin addini da na boko.

A nan ne aka sami wata yarinya ‘yar shekara 14 da ake kira Asma'u Dauda, wadda ta ki yarda ayi saurin yi mata aure, inda ta zabi neman ilimin boko tukunna.

Asma’u ta ce ta ki amincewa da a yi mata auren wuri don ta yi karatun boko, saboda ta gano cewa karatu yana da muhimmanci sosai a rayuwa. Yanzu haka kuma ta fara karatun na boko.

Ta ce abin da ya bata kwarin guiwa shine yadda aka fara koyar da su karatu a makarantar su ta islamiya kuma suna gane abin da ake koyar da su.

"Buri na shi ne in zama likita," in ji Asma'u, wadda yanzu ta kai aji 4 na sakandare.

Makarantar Allo da ake hadawa da karatun boko
Makarantar Allo da ake hadawa da karatun boko

Jami'in da ke aikin kula da yadda ake koyar da karatun boko ga daliban makarantun islamiya, Aminu Bello Danchadi, ya ce wannan tsarin ya taimaka wajen gano yara masu hazaka kamar Asma'u, wadda ta sami hawan turbar cimma burinta na neman ilimi bayan ta ki aminta ayi saurin yi mata aure.

Ya ce kowane karshen zangon karatu yana bibiyar sakamakon karatun ta, kuma tana nuna hazaka sosai, har makarantar da take ta nemi iyayenta da su barta ta cimma burin rayuwarta na zama ma'aikaciyar lafiya.

Ya kara da cewa "an nemi iyayenta da kada su yi mata aure ko bayan ta kammala sakandare saboda an lura tana da hazaka sosai kuma tana iya kawo ci gaba ga al’ummar ta."

"Wannan babban darasi ne yarinyar ta nuna," a cewar Sakataren Ilimi na yankin Bodinga, Lawali Na’akka Mu’azu, yana mai cewa "abin koyi ne ga sauran ‘yan mata har da iyayen yara."

Ya ce da ma ilimin mata yana da muhimmanci sosai fiye da na maza, akan haka ya ji dadin samun wannan yarinya wadda idan ta ci gaba da karatu za ta sami nasarar rayuwa har ma ta taimaki al'ummar ta.

Shugaban hukumar ilimin firamare da karamar sakandare a jihar Sakkwato, Altine Shehu Kajiji, ya ce Ilimin ‘ya'ya mata yana samun kulawa sosai daga gwamnati da ma masu bayar da tallafi na kasashen duniya.

Ya ce sun fahimta cewa idan aka hana mata damar neman ilmi, to ba za'a sami irin ci gaban da ake sa ran a samu ba a cikin kowane al'umma.

A Najeriya dai gwamnatoci da wasu hukumomi na duniya sun dade suna fafutuka kan habaka sha'anin ilimin ‘ya'ya mata da rage auren wuri ga ‘yan mata, kuma fafutukar na ci gaba da samun karbuwa a wasu jihohin kasar.

Samuwar wannan yarinya Asma'u Dauda, ya nuna kwalliya ta soma biyan kudin sabulu.

A can baya ana daukar yankin arewacin Najeriya a zaman wanda aka tserewa ta bangaren ci gaban ilimin zamani, sai dai biyowa bayan fafutukar da hukumomin ke yi yanzu labarin yana sauyawa.

Wannan kokarin ya sa shima Ilimin ‘ya'ya mata yanzu yana samun bunkasa har a jihohin da tasirin al’adu da addini ke kange ‘yan mata daga karatun boko, inda yanzu ake gwama ilimin boko da na addini a makarantun allo da Islamiya.

Daga cikin hukumomin da ke tallafawa ilimin ‘yan mata a Najeriya akwai Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dunkin Duniya UNICEF wanda ke gudanar da aiki a jihohi 6, ciki har da Sakkwato karkashin tallafin Babban ofishin kasashe renon Ingila mai kula da kasashen ketare wanda kuma kwalliya ta biyan kudin sabulu a bangaren ilimin ’ya ‘ya mata.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG