Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau juma'a aka shirya za'a rantsar da sabon shugaban Ivory Coast


Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara a birnin Abidja.
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara a birnin Abidja.

Hukumar lura da kundin tsarin kasar Ivory Coast tace a yau juma'a za'a rantsar da Alassane Ouattara a zaman shugaban kasa. A jiya kotun kolin kasar ta ayyana Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a bara.

Hukumar dake lura da kundin tsarn mulkin kasar Ivory Coast tace a yau juma'a za'a rantsar da Alassane Ouattara a zaman shugaban kasar. A jiya Alhamis kotun kolin kasar ta yanke hukuncin ayyana cewa Mr Ouattara ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a bara da kashi hamsin da hudu daga cikin dari na kuri'un da aka kada. Matakin daya kauda hukuncin da wata kotu ta yanke cewa tsohon shugaba Lauren Gbagbo shine ya lashe zaben. Mr Gbagbo yayi amfani da hukuncin farko ya makalewa jan ragamar mulkin kasar. Kiyawar da yayi na sauka daga kan mulki ya hadasa tarzomar watani hudu ta fafitukar iko data zama sanadin mutuwar daruruwan mutane kuma imamin mutum miliyan guda suka rasa matsuguninsu. A watan jiya Mr Ouattara ya dare kan ragamar mulki bayan da magoya bayansa suka kama bijirerren Mr Gbagbo a gidansa dake birnin Abidjan tare da taimakon sojojin Majalisar Dinkin Duniya dana kasar Faransa. A wani labarin kuma a jiya Alhamis Amirka tace zata baiwa kasar Ivory Coast karin taimakon dala miliyan takwas da rabi domin taimakon wadanda suka arce daga gidajensu a sakamakon rikicin siyasar da aka yi a kasar. Jami'an Amirka sunce za'a yi amfani da udin wajen samar da ruwa da magunguna da kuma wasu kayayyakin masarufi.

XS
SM
MD
LG