Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami gawarwakin mutane sittin a wani birnin kasar Ivory Coast


Yan gudun hijirar kasar Ivory Coast suna sauke kayansu a filin wasan Ouagadougou, Burkina Faso
Yan gudun hijirar kasar Ivory Coast suna sauke kayansu a filin wasan Ouagadougou, Burkina Faso

Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross sun ce an gano gawarwakin a kalla mutane 60 a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast yayinda gwamnati ke kokarin shawo kan gyauron mayakan dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo

Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross sun ce an gano gawarwakin a kalla mutane 60 a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast yayinda gwamnati ke kokarin shawo kan gyauron mayakan dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo. Kungiyar agajin tace, an sami da dama daga cikin gawarwakin ne a birnin kasuwanci na Yopougoun, inda dakarun gwamnatin suka yi arangama da mayakan dake goyon bayan Gbagbo ranar Talata. Gwamnatin shugaba Alassane Quattara na kokarin maido da zaman lafiya da kuma tsaro a kasar dake yammacin Afrika bayan an shafe watanni ana fama da rudamin siyasa. An shiga tashin hankali ne sakamakon kin mika mulki da Mr. Gbagbo yayi bayan sanar da Mr. Quattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Nuwamba. Mr. Quattara ya hau karagar mulki watan jiya bayanda magoya bayansa tare da taimakon dakarun MDD da na kasar Faransa suka kama Mr. Gbagbo a gidansa. Rudamin shugabanci tsakanin mutanen biyu ya yi sanadin mutuwar daruruwan farin kaya yayinda sama da mutane miliyan daya suka kauracewa matsugunansu.

XS
SM
MD
LG