Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Wakilai A Amurka Zasu Kada Kuri'ar Tabbatar Da Donald Trump


Yau Littinin ne za a bude babi na karshe na zaben shugaban kasar Amurka wanda zai tabbatar da zaben da aka yi.

Domin a yau din ne ake sa ran wakilai zasu tabbatar da zaben da aka yi wa hamshakin mai kudin nan, sananne a harkar gine-ginen gidaje, cewa ko shi ne zai zama shugaban Amurka na 45.

Tun a farkon watan Nuwamba sun san cewa Donald Trump shine zai karbi ragamar mulkin Amurka bayan an rantsar dashi a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa.

Sai dai kuma zaben Amurka ba ya kammala da zaben gama gari, amma dana sakamakon wasu daidaiku na zaben shugaban kasa a jahohin kasar 50 hadi da babban birnin tarayya dake birnin Washington.

A bisa tsari wanda yafi samun kuri’u mafi rinjaye a akowace jaha shine ke samun daukacin wakilai, wanda ake bayar da yawan kuri’unsu kwatankwacin yawan jama’ar da suka jefa kuriar su a wannan jahar.

Yanzu dai a yau wakilan su 538 zasu jefa kuri’arsu a hedikwatocin jahohinsu.

‘Yar takarar jamiyyar Democrat, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta zarta Trump da kuri’u miliyan 2.9 a zaben kasa baki daya. To amma sai dai Trump din ya fita samun nasara a jihohin da suka fi tasiri.Domin ko ya samu wadatattun kuri’u har 306 sama da 270 da ake bukatar ya samu na wakilai.

XS
SM
MD
LG