Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za a Bude Babbar Kasuwar Garin Kaduna


Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa
Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

Bayan kwashe sama da watanni hudu da kulle kasuwanni da guraren ibada a jahar Kaduna, gwamnatin ta bada sanarwar bude babbar Kasuwar Kaduna wato 'Central Market' a matsayin gwajin bin dokar komawa kasuwannin Kaduna.

Tun bayan billar cutar Korona a Najeriya gwamnatin Kaduna ta rufe kasuwannin da saka dokar zaman gida wanda wasu su ka dinga kokawa da irin hadin da al'uma ta shiga

A jiya Alhamis ne dai aka sa ran bude Kasuwannin na Kaduna amma shugaban hukumar kula da kasuwannin jahar Kaduna malam Hafiz Bayero ya ce an dage zuwa yau Juma'a ne don kammala shirye-shirye. Ya kuma bayyana cewa, ba za a bari wanda bashi da takunkumi ya shiga kasuwar ba.

Ko bayan Kasuwanni ma akwai yiwuwar gwamnatin Kaduna ta bude wuraren ibada don gudanar da salloli biyar na kullum maimakon Juma'a kadai da ake yi a yanzu. da kuma ayyukan ibada na kiristoci.

Sakataren majalissar malamai da limamai ta jahar Kaduna, Malam Yusuf Yakub Arrigasiyyu ya yiwa manema labarai Karin bayani jim kadan bayan wani taro manyan malamai da gwamnatin Kaduna ta kira. Bisa ga cewarsa shugabannin addinan sun bada shawarwari kan yadda za a koma gudanar da ayyukan ibada kamar yadda aka saba ba tare da fadawa cikin hadarin kamuwa da cutar ta Coronavirus ba.

Kasuwar Garki, Abuja
Kasuwar Garki, Abuja

Gudun ketara dokokin da gwamnati ta shimfida don bude kasuwannin ya sa kungiyar 'yan Kasuwan jahar Kaduna kiran wani taro inda shugabannin kungiyar suka ja hankalin membobinsu kan hanyoyin da za a kiyaye dokokin da gwamnati ta gindaya

Salon yaki da cutar Korona a jahar Kaduna dai ya sha suka daga wasu 'yan jahar Kaduna, kamar irin su Alh. Sani Sa'ad Sufi Wanda ya bayyana takaicin yadda gwamnati ta ce tana kashe naira miiyan guda kowacce rana wajen jinyar wadanda suka kamu da cutar a yayinda sauran al’umma suke fama da yunwa.

Ana sa ran dai idan 'yan-kasuwar jahar Kaduna sun ci jarabawar bude babbar Kasuwar Centra a yau Juma'a, za a bude sauran kasuwanni sannu a hankali.

Saurari rahoton Isa Lawal Ikara cikin sauti

Yau Za a Bude Babbar Kasuwar Garin Kaduna:3"25"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG