Accessibility links

Muna da Kayan Aiki – inji Jami’an Tsaron Najeriya


Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Chris Olukolade wanda ya bada sanarwar ceto mafi yawancin daliban Cibok, daga baya kuma ya janye wadannan kalamai.

Jami’an tsaron Najeriya sunce suna da isassun kayan aiki na amfani da su wajen neman daruruwan dalibai mata wadanda aka sace daga makarantarsu ta Sakandare a Cibok.

Misalin shekaru 20 da suka wuce, duniya ta kalli dakarun sojin Najeriya a matsayin karfin soji mai wanzar da zaman lafiya a kasashen yammacin Afirka. Sai dai a halin yanzu Najeriyan tana fama wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin iyakokinta, yayinda mayakan sa kai a arewa maso gabashin kasar suke kashe dubban mutane.

An yi watsi da horo da atisaye, sannan ba’a kulawa da lafiyar kayan aiki, musamman ma na’urar “Radio” wadda jami’an tsaro ke amfani da shi wajen ganawa, suma babu isassu.

Rashin lura da horo, da kuma gazawa wajen kula da kayan aiki, da ma rashin baiwa kasashen yammacin duniya hadin kai ya lalata dakarun sojin Najeriya, a dai-dai lokacin da take fuskantar mayakan sa kai wadanda ke da manyan lafiyayyun makamai.

Yayin da duniya take zubawa dakarun Najeriya idanu domin gani ko ta yaya zasu kwato daliban mata su sama da 200 wadanda aka sace ran 14 ga watan Afrilu, har yanzu sojojin Najeriya basu da tabbacin inda suke, amma sun dage akan cewa zasu iya nemo daliban.

Kakakin ma’aikatar Tsaro, Chris Olukolade ya gana da manema labarai akan inda aka kwana.

“Dakarun JTF wadanda suka hada da na kasashen dake makwabtaka da Najeriya, an kaddamar da su, domin su mayar da hankulansu wajen neman yaran,” a cewar Olukolade.

“Kamar yadda kuka sani, JTF na da rashe a Cadi, da Nijer, duk da cewa sojojin Najeriya sunfi yawa a cikinta, saboda haka duk zamu mayar da hankula ne akan bakin iyakokin Najeriya da Nijer, inda zamu ringa ganawa domin raba bayanai idan muka ga daliban.”

Kakakin ‘yan Sanda farin kaya, wato SSS Marilyn Ogar tayi kira ga ‘yan Najeriya akan su mika bayanai ga jami’an tsaro idan suka ga wani abu.

“Mun yi kira akan cewa sai ‘yan Najeriya sun lura da tsaro, kuma sai suna lura da inda suke, saboda idan muka ce muna kan kowace hanya, ba dai-dai mukeyi ba, kuma ba anan kawai muka tsaya ba, mun samar da lambobin tsaro kuma muna so muce ‘yan Najeriya sun taka rawar gani,” a cewar Ogar.

Kasashe da dama, a ciki harda Amurka, Britaniya, Faransa, da Sin duk sunce zasu taimakawa Najeriya wajen samo daliban. Kwararru daga Britaniya a cikinsu, harda jami’an diflomasiyya, da jami’an agajin jin kai, da ma jami’an Ma’aikatar Tsaro sun isa Najeriya Juma’arnan domin baiwa gwamnati shawara dangane da neman daliban.
XS
SM
MD
LG