Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Ya’yan PDP su 3000 Sun Koma APC


APC
APC

Kimanin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP dubu uku ne suka canza sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC a jihar Neja dake tarayyar Najeriya.

Ko da yake dai shugabannin PDPn a yankunan da wadannan mutane suka fice sunce “Allah Ya raka taki gona”, manazarta harkokin siyasar Neja sun hango wa jam’iyyar PDP illa, bisa la’akari da muhimman mutanen da suke ficewa daga jam’iyyar a halin yanzu.

Alhaji Yakubu Abubakar kani ne ga tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar, wanda ya mika wa jam’iyyar PDP mulki a shekara ta 1999, shine jagoran wadannan mutane sama da dubu uku da suka bar PDPn a yanzu, ya bayyana dalili.

Yace “kamar yadda mutane suke fita, yana daga cikin abunda ya kara mana karfin gwiwa, muka ce muma bari mu fita. Saboda in ka lura, zaka ga cewa akwai ‘yan majalisar Wakilai da suka fita, akwai kuma gwamnoni da suka fita”.

Jihar Neja dai, jiha ce mai salon bin jam’iyyar guda kwai da kwarkwata, sai dai dan abunda ba za’a rasa ba.

Sai dai da alama wannan karan abun zai sha bam-bam, bisa la’akari da yadda jamiyyar APC take daukar baki.
XS
SM
MD
LG