Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Ci Gaba Da Shari’ar Bukola Saraki Har Sai An Kai Karshe


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, a gaban Kuliya

Yau Litinin ne 18 watan Afrilu shugaban Majalisar Dokon Najeiya Bukula Saraki ya sake gurfana a gaban Alkali Dan Ladi Umar.

To sai dai lawyan gwamnati da yake tuhumar Bukula Saraki, bai bayyana ba kan lokaci da ya kamata ya gabatar da shi domin ci gaba da wannan shari’a, hakan yasa a ka ‘daga lokacin sauraron zuwa karfe daya na rana agogon Najeriya.

Yanzu haka dai an fara wannan shari’a kuma za a ci gaba babu sassautawa har sai an gama shari’ar an yanke hukunci a kotun da’ar ma’aikata.

Abin da yafi daukar hankali kan wannan shari’ar shine yawancin Sanatoci dake yiwa Bukola rakiya suna goyon bayansa a lokacin da aka fara wannan shari’a, sun jaye basu da yawan da suke a farkon shari’ar.

Domin karin bayani Saurari Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG