Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Jarraba Bin Sabuwar Hanya Wajen Sake Gudanar da Zaben Gwamnan Jihar Anambra a Karo na Uku


Wani mutum yana kada kuria a zaben majalisar tarayya

A karshen mako ne ‘yan Nigeria zasu sake kada kuri’unsu a karo na uku wajen bin sabon tsarin zaben Gwamna a karon farko tun hadewar da jam’iyyun siyasa suka yi.

A karshen makon nan ne wasu ‘yan Nigeria ke zuwa rumfunan zabe domin sake kada kuri’unsu a zagaye na uku, na jarraba bin sabuwar hanyar zaben da aka shirya a zagayen farko na zaben Gwamnoni tun hadewar da jam’iyyu suka yi domin yin takarar zabe.

Masu fashin bakin al’amuran da suka jibanci zabe sun fadi cewar maimakon sabbin jam’iyyu su nuna irin farin jinin da suke dashi, rashin gudanar da zaben kamar yadda ya kamata, ya nuna cewar hukumomin zabe a Nigeria basu shirya yadda ya kamata ba domin fuskantar zabukan da za’a gudanar a shekarar 2015, zaben da zai hada harda na shugaban kasa.

Makonni biyun da suka gabata ne tun farko aka shirya gudanar da zaben Gwamna a jihar Anambra, zaben da ake ganin shine irinsa na farko tun afkuwar matsalar rarrabuwar da aka samu a jam’iyyar PDP dake mulkin Nigeria, da hakan ya haifar da jam’iyyun hamayya hudu. Inda sakamakon zaben a kudancin Nigeria ya nuna irin karfin goyon bayan da shugaba Goodluck Jonathan ke dashi, da kuwa ana iya hassashen samun matsala a babban zaben da za’a gudanar a shekarar 2015.

Amma duk da haka, ana iya cewa an koyi wani darasi daga gudanar da zaben shi kansa. Anji jami’in fashin bakin al’amuran siyasa Anthony Chigbo na fadin cewa, bacewar kuri’u da samun jinkirin fara zaben cikin lokaci da bacewar sunayen masu kada kuri’a a rajistar masu zabe duk sun janyo cikas wajen kammala zaben kamar yadda ya dace. Domin kwana guda bayan zaben, masu kada kuri’a sun sake komawa rumfunan zabe don sake kada kuri’unsu, amma sai ya kasance ita kanta hukumar zaben bata shirya ba.

Yace jami’an hukumar zabe sun gaza hana ‘yan siyasa yin amfani da kudi domin sayen kuri’a. An sayi kuri’a a zaben Anambra kan kudi Dalar Amurka $25 a dukkan ranaikun da aka gudanar da zaben. Chigbo yana mai cewa ga dukkan alamu dai fatara da talauchi ne suka haifar da matsalar saida kuri’a a lokacin zabe,akwai kuma jahilcin rshin sanin halin zaman rayuwa, wasu basu da cin yau balle na gobe.

A shekarar 2011 idan za’a tuna, tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan bayyana sakamakon zaben shine asarar rayukan mutane sama da 800 a Nigeria, kuma tun daga lokacin al’amura sai kara rinchabewa suke yi. Daga karshe Chigbo yace yayi mamaki kwarai da ganin irin yadda hukumomin zaben jihar Anambra suka kasa yin kyakkyawan shiri domin tinkarar zabe irin wannan.
XS
SM
MD
LG