Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Koma Yin Shari'ar Ta'addanci A Asirce – Babbar Kotun Najeriya


A ranar Alhamis ne wani alkalin kotun tarayya ya yanke hukuncin cewa, daga yanzu za a ci gaba da gudanar da dukkan shari’ar ta’addanci a Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani wato ta amfani da bidiyo da kuma ta kafar sadarwa ta intanet.

Alkalin babbar kotun tarayya a Najeriya, John Tsoho ya fitar da wata sanarwa mai taken "sabbin shawarwarin aiki kan sauraron kararrakin ta'addanci" da ke bayyana yadda kotun za ta rika gudanar da shari'un da suka shafi ta'addanci a gaban kotun.

Ya ce an tsara sabon hukuncin ne domin tabbatar da tsaron dukkan bangarori, daga masu laifin da ma jama’a da kuma tabbatar da adalci.

A gefe guda kuma, jagoran haramtacciyar kungiyar 'yan awaren da ake zargi da laifukan ta'addanci ya shigar da kara yana zargin cewa ba za a iya yi masa shari'a ba saboda an tasa keyar sa daga Kenya ba bisa ka'ida ba, kamar yadda takardun kotu suka nuna.

Nnamdi Kanu shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ya bace ne daga Najeriya bayan ya tsallake beli a shekarar 2017.

An kama shi bayan shekaru da dama yana gudu. Lauyansa ya ce a shekarar da ta gabata an zalunce shi a tsare a Kenya kafin a mayar da shi Najeriya, lamarin da Babban kwamishinan na Kenya ya musanta.

Lauyan Kanu, Mike Ozekhome, a ranar Alhamis, ya ce ba za a iya yi masa shari’a kan zargin ta’addanci da yada labaran karya da sane ba saboda ba a mika shi ga Najeriya ba bisa wadannan tuhume-tuhumen.

Ozekhome yana rokon kotu da ta bayyana tsare shi a matsayin haramtacciyar doka. Har ila yau karar na neman diyyar naira biliyan 50 (dala miliyan 120) da kuma naira miliyan 100 na kudaden shari’a.

A ranar Juma’a ne ake sa ran wata kotu na daban za ta yanke hukunci kan tuhume-tuhume 15 da ake tuhumar Kanu, wadanda za su iya kawo karshen shari’arsa idan har alkali ya amince da bayannan na lauyansa.

Kanu bai yarda da duk wasu tuhume-tuhumen da ake masa ba.

Kungiyar IPOB, wacce Kanu ya kafa a shekarar 2014, na neman ballewar yankin kabilar Igbo, wadda ta mamaye yankin kudu maso gabashin Najeriya. Hukumomi suna kallon IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci. IPOB ta ce tana son samun 'yancin kai ne ta hanyoyin da ba na tashin hankali ba.

XS
SM
MD
LG