Accessibility links

Za A Yi Aiki Da Shari'ar Musulunci Wajen Zana Sabon Tsarin Mulki A Libya


Shugaban gwamnatin wucin gadin Libya, Mustafa Abdel Jalil, yana ayyana 'yantar da kasar Libya daga mulkin Gaddafi, lahadi 23 Oktoba 2011 a birnin Benghazi.

Shugaban wucin gadi yace za a kuma dage dokar da ta kayyade yawan matan da mazajen Libya zasu iya aure

A wurin wani bukin da dubban mutane suka halarta a birnin Benghazi dake gabashin Libya, shugabannin wucin gadi na kasar sun ayyana ‘yanto ta daga mulkin shekaru 42 na marigayi Muammar Gaddafi.

Shugaban Majalisar Mulkin Wucin Gadi, Mustafa Abdel-Jalil ya fadawa gungun mutanen da suka hallara cewa za a yi amfani da tsarin shari’ar Musulunci wajen gina harsashin sabon tsarin mulkin da za a yi amfani da shi a bayan mulkin Gaddafi. Yayi alkawarin cewa za a kakkafa bankunan Islama, sannan kuma za a soke dokar da ta kayyade yawan matan da mazaje a kasar Libya zasu iya aura.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya bayyana ayyana ‘yantar da Libya a zaman wani lokaci na tarihi bayan mulkin kama-karya na shekara da shekaru. A cikin sanarwar da ya bayar jiya lahadi, Mr. Ban ya sake jaddada goyon bayan Majalisar ga matakan da gwamnatin wucin gadi ta ke dauka na kafa gwamnatin rikon-kwarya tare da gudanar da zabe.

Firayim ministan wucin gadi na Libya mai barin gado, Mahmoud Jibril, yace ana tuntubar sassa da nufin kafa sabuwar gwamnatin rikon-kwarya nan da wata daya, daga nan sai a gudanar da zaben majalisar zana sabon tsarin mulki cikin watanni 8. Za a gudanar da zabubbukan majalisar dokoki da shugaban kasa cikin shekara guda a bayan kafa majalisar zana tsarin mulkin.

Jibril ya bayyana wannan ne a gefen wani taron tattalin arziki da ake yi a kasar Jordan, inda ya bayyana yin murabus dinsa domin bai wa sabbin shugabanni damar jan ragamar kasar Libya zuwa ga tafarkin dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG