Accessibility links

An jinkirta jana'izar Moammar Gaddafi

  • Jummai Ali

Tsohon shugaban Libya Moammar Gaddafi, kafin ya mutu.

Jami’an gwamnatin rikon kwaryar Libya sun jinkirta shirye shiryen jana’izar tsohon shugaba Moaamar Gaddafi a yau juma’a, kwana daya bayan an kashe shi a lokacinda mayakan yan tawaye suka kutsa garinsu Sirt. Tunda farko jami’an sunce za’a bizne Gaddafi a yau juma’a a wani wurin wuri da ba'a baiyana ba.

Jami’an gwamnatin rikon kwaryar Libya sun jinkirta shirye shiryen jana’izar tsohon shugaba Moaamar Gaddafi a yau juma’a, kwana daya bayan an kashe shi a lokacinda mayakan yan tawaye suka kutsa garinsu Sirt. Tunda farko jami’an sunce za’a bizne Gaddafi a yau juma’a a wani wuri da ba'a baiyana ba.

To amma kuma kafofin yadda labaru sun ambaci jami’an hukumar mulkin wucin gadi ta kasar da ake cewa NTC a takaice, suna fadin cewa za’a jinkirta yin jana’izar tsohon shugaban, a saboda rashin sanin ainihin inda za’a bizne shi da kuma yiwuwar binciken kotun kasa da kasa.

Kamfanin dilancin labarun Reuters ya bada labarin cewa gwamnatin rikon kwarya tana nazarin zabin baiwa yan kabilar Gaddafi gawarsa domin suyi masa jana’iza.

A halin da ake ciki kuma, ofishin nazarin kare hakkin jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da binciken mutuwar Gaddafi. Mai magana da yawun ofishin, Rupert Colville ya fada a yau juma’a cewa har yanzu ba’a tantance yadda tsohon shugaban ya mutu ba, kuma hoton vidiyon gawarsa da ake nunawa yana tada hankali.

Ana dai ci gaba da baiyana ra’ayi akan mutuwar Moammar Gaddafi. Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton tace mutuwar Gaddafi ta rufe babin takaici a tarihin kasar Libya, kuma ta zama mafarin bude sabon babi a kasar.

Yau juma’a Mrs Clinton tayi wannan furuci a kasar Pakistan, kwanaki uku bayan ta kai ziyara Libya a ziyarar kasashen gabas ta tsakiya da kudancin Asiya da take yi.

Itama kasar China a yau juma’a tace, Libya ta bude wani sabon babi a rayuwarta kuma tayi kira ga shugabanin gwamnatin rikon kwaryar kasar da su fara shirin siyasar da zai kunshi ko kuma wakiltar dukkan bangarorin kasar.

A nata bangaren, a yau juma’a kasar Afrika ta kudu, a yau ta baiyana fatar abubuwan da suke faruwa a Libya zasu zama sanadin ganin bayan zaman gaba, a maido da zaman lafiya a kasar. Iran tace, tana fatar za’a kawo karshen yakin basasa a kasar, a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG