Accessibility links

Za'a Gudanarda Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano Wannan Watan


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Tun watan Satumba bara hukumar zaben jihar Kano ta fitar da jadawalin zaben kananan hukumomi da zata yi wannan watan.

Tun shekarar da ta gabata hukumar zaben jihar Kano ta fitar da jadawalin zaben kananan hukuma da yadda zata aiwatar da zaben.

Jadawalin ya nuna za'a yi zaben cikin watan Maris na wannan shekarar. Hukumar zata rufe karbar sunayen 'yan takara ranar 13 na wannan watan. To saidai kawo yanzu jam'iyyar ACPN ce kadai ta bayar da sunayen 'yan takara a kananan hukumomi biyar cikin 44.

Alhaji Ismaila Idris Garba kwamishanan hulda da kafofin yada labarai na hukumar zaben. Yace cikin jam'iyyu 17 daya tak ta mika sunanyen 'yan takara a kananan hukumomi 5 alhali kuwa hukumar zata dakatar da karbar sunaye ranar 13 ga wannan watan. Dangane da ko zasu karawa jam'iyyu lokaci sai yace idan yin hakan bai sabawa kundun tsarin zaben ba zasu kara. Idan kuma ya sabawa kundun tsarin to shi ke nan.

Ban da rashin mika sunayen 'yan takara, babu kuma hada-hada irin ta siyasa da aka saba gani idan akwai zabe kamar yadda aka saba can baya.

Masu fashin baki a fannin siyasa sun fara tofa albarkacin bakinsu game da lamarin. Malam Albaci Bako daraktan cibiyar kasa da kasa da bincike kan nazarin siyasa da dimokradiya a Kano yace rashin hada-hada kamar yadda aka saba kila yana da nasaba da tattalin arziki. Abu na biyu kuma tana yiwuwa ita hukumar zaben bata wayar da kawunan mutane ba kamar yadda ya kamata ta yi. Watakila kuma gwamnan jihar yana tsoron kada wasu rigingimu su taso da zasu shafi jam'yyarsa.

Tun shekarar 2010 kananan hukumomin 44 suke karkashin kantomomi.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG