Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Najeriya: Hada-hadar Harkokin Siyasa Sun Fara Kankama


Sarakunan Gargajiya A Jihar Adamawa Sun Bukaci Hukumar Zabe Ta Kara Azama
Sarakunan Gargajiya A Jihar Adamawa Sun Bukaci Hukumar Zabe Ta Kara Azama

Yayin da ya rage ‘kasa da watanni bakwai a gudanar da babban zabe a Najeriya, hada hadar harkokin siyasa sun fara kankama, ta hanyar gudanar da tarukan magoya baya da kuma neman kuri’ar zaben cikin gida na fitar da gwani.

Tarukan neman kuria’ar delegate da masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam’iyyar hamayya ta PDP da kuma gangamin da hadiman shugaba Muhammadu Buhari keyi a jihohi domin jaddada goyon baya na daga cikin manyan batutuwan da ke daukar hankali a fagen siyasar Najeriya.

Ko a ranar Asabar din nan, sai da guda cikin mukarraban shugaba Muhammadu Buhari a Kano, Janar Lawal Jafaru Isa, ya yi gangamin hadin kan magoya bayan shugaban, inda har-ma ya nanata cewa, Kanawa masoyan Buhari ne kuma shugaban ya yi musu tanadi na musamman.

Hakan na zuwa ne, a dai dai lokacin da manyan sabuwar APC irin su tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki, ke ci gaba da tsare-tsaren fita daga jam’iyyar ta APC mai mulki, duk da lallashin su da shugabancin jam’iyyar keyi.

A daya bangaren kuma, masu neman takarar shugabancin Najeriya a PDP na kara ‘kaimi wajen neman kuri’ar Delegates, domin tunkarar babban taron jam’iyyar na fidda gwani wadda zai wakana a cikin watan gobe na Agusta.

A rannar Asabar din nan ce shi-ma Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da ta sa takarar a karkashin lemar ta PDP a garin Yolan jihar Adamawa.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG