Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN NIJAR: Nakiya Ta Hallaka Jami'an Zabe 7 a Yankin Tillaberi


'Yan bindiga sun hallaka faransawa 6 da 'yan Nijar 2 a gabashin Niamey

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun tabbatar da rasuwar wasu jami’an zabe bakwai kana uku suka ji rauni a ranar Lahadi 21 ga watan Faburairu.

Hadarin ya auku ne bayan da motarsu ta taka nakiya a kauyen Dargol da ke yankin Tillaberi iyakar kasar ta Nijar da Burkina Faso.

A wata hira ta wayar tarho gwamnan jihar Tillaberi, Tidjani Ibrahim Katchiella, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da wadannan jami’ai ke kokarin isa rumfunar zabe.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen Sahel masu fama da hare haren ta’addanci ta bangaren jihohin Tillaberi da Tahoua bayan da kungiyoyin ‘yan bindiga suka tare a arewacin Mali a shekarar 2012.

Yayin da kuma kungiyar Boko Haram ke kai farmaki akai akai a jihar Diffa da ke yankin kudu maso gabashin kasar da ke iyaka da Tarayyar Najeriya.

Tabarbarewar tsaro a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina inda masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da barayin shanu ke sheke ayarsu wata matsala ce da ta shafi kasar ta Nijar ta bangaren jihar Maradi.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG