Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAMFARA: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane 60 A Wani Sabon Hari


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 60 a wani yanki mai nisa a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya wadanda galibinsu mata ne masu gudanar da Maulidin Annabi Muhammad, kamar yadda mazauna jihar suka bayyana jiya Alhamis.

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi kaca-kaca da yankin arewa maso yammacin kasar inda suke yin fashi ko kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, kuma tashe-tashen hankula na karuwa ganin yadda jami'an tsaro masu karamin karfi suka kasa dakile hare-haren da ake kaiwa.

Hakan dai ya haifar da fargabar ko mazauna yankin za su iya kada kuri’a a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairu domin zaben wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari, wanda tsarin mulkin kasar ya haramtawa sake tsayawa takara.

Wasu mazauna garin biyu sun ce wasu ‘yan bindiga a kan babura ne suka isa unguwar Magami Tandu da ke karamar hukumar Kaura Namoda a yammacin Laraba inda suka yi ta harbe-harbe.

Sun dauki galibin mata ne da suke gudanar da bukin Maulidin Manzon Allah SAW wanda ake gudanarwa tsakanin karshen watan Satumba zuwa karshen watan Nuwamba a jihohin Musulmin Arewacin Najeriya, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

A kullum ana kashe-kashe ko sace-sacen mutane, wanda hakan ke sa mu mu rasa mazaunin mu. Don Allah ku gaya wa gwamnati ta yi mana adalci.” Inji Abdulkarim Haruna, wanda shi ma aka yi garkuwa da matarsa.

Mazauna garin sun ce an kashe mutane 19 a ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Ryuji da ke karamar hukumar Zurmi ta Zamfara, da ke makwabtaka da Kaura Namoda.

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu ba, domin jin ta bakinsa.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG