Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu taimakawa Najeriya wajen yaki da Boko Haram - Samantha Power


Samantha Power jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) wadda shugaba Obama ya tura zuwa Najeriya

Yayinda ta gana da masu gwagwarmayar ganin an sako 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata, Samantha Power ta sake jaddada matsayin Amurka tana cewa ba zasu yi kasa s gwuiwa ba wajen taimakawa Najeriya a yakinta da Boko Haram

Samantha Power tace sun dage sai sun ga an kwato 'yan matan Chibok don maidasu wajen iyayensu.

Tun farko Jakadiyar ta gana da kungiyoyi masu zaman kansu da na addini inda batun tasirin taron majalisar musulunci ta duniya da aka yi kwanan nan a Abuja ya taso. Makasudin taron shi ne don kara ilimantar da musulmi illar 'yan ta'ada dake fakewa da sunan addinin musulunci suna zubar da jinin mutane ba tare da hakkin shari'a ba.

Haka ma taron ya nisanta musulunci da duk wata alaka da Boko Haram.

Fatima Bukar daya ce daga shugabannin gwagwarmayar kwato 'yan Chibok tace Samantha Power jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya tana Najeriya ne da yawun shugaban Amurka Barack Obama. Tace zuwanta tabbaci ne garesu cewa duk abubuwan da suke yi suna bisa hanya ne.

Da ta juya kan yaran da suka kubuta daga hannun Boko Haram tace yaran suna neman taimako domin wasunsu sun ga an kashe iyayensu a gabansu. Wasu kuma an ci zarafinsu yayinda suke hannun Boko Haram. Ko a fannin lafiyar jikinsu suna bukatar taimako. Tace lamarin ya fi karfin gwamnati sai kasashen duniya sun taimaka. Yadda kasashen duniya suka tashi akan Syria haka yakamata su yiwa Najeriya.

Wata Malama Abigail da 'yaruwarta Monica da suka kubuto daga hannun Boko Haram daga garin Gwoza suka shiga har Kamaru kafin isowa sansanin 'yan gudun hijira na Abuja tace Monica ta sadu da 'yan matan Chibok a dajin Sambisa inda Boko Haram ke cin zarafin matan.

Monica tace da dare suka isa Sambisa ta hanyar Bama. Tace ana basu abinci amma kowace rana namiji daya sai ya tara da mata goma sha biyar. Tace akwai wasu fararen mutane da dama tare da 'yan Boko Haram din. Ana tanada masu kowane irin abinci. Idan rabinsu sun je yaki sai rabi kuma su kwana da matan da aka kama.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG