Ziyarar da shugaba Jacob Zuma na kasar Afrka ta kudu ya kai Jihar Imo kudu maso gabashin Najeriya ta bar baya da kura a yayinda dangantakar Najeriya da Afrika ta kudu take kara tabarbarewa .
Yanzu dai ana sukar lamirin gwamnatin Jihar Imo, karkashin jagorancin Rochas Okorocha wacce ake zargi da kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan dari biyar da ashirin, wajen karbar bakuncin Jacob Zuma da tawagarsa da kuma gina mutunmutumin shugaban.
Jama’a sunyi Allah wadai tare da cewa wannan abin takaici ne ganin yadda gwamnatin ta ware makudan kudade dan karrama shugaba Jacob Zuma alhali ya kamata ta maida hankali wajen aiyuka na gari da zasu kara taimakawa al’ummar.
Muryar Amurka ta zanta da wasu wanda sukai tsokaci akan batun suna cewaabinda Rochas Okorocha yayi baida ma’ana domin Naira miliyan dari biyar da ashirin zai iya fitar da mutane dari biyar da ashirin daga talauci ya kuma basu sana’a a cewar Nnamdi Orji.
Karrama wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa ya nuna karrama gazawa da kuma shirme inji Emeka.
Muhammad Bulama yace wannan barnar kudi ne, ga mutane suna wahala a garin ya kamata gwamna yayi masu abinda ya kamata ga ayyuka nan an fara duk ba a gama ba , Ibrahim ma mazaunin imo yace suna rokon a maida hankali a wajen ayyukan gari kamar shataletale da aka fara ba a gama ba ga tituna ba a gama ba don haka a dauki irin wannan kudaden a karasa ayyukan.
Facebook Forum