Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Mataimakin Shugaban Najeriya Birnin Kano


Yemi Osinbajo Ya Kai Ziyara Kano Don Dubba Shirin Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Da Wasu Ayyukan

Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar aiki birnin Kano, inda ya tabbatar da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa 'yan kasuwa da kananan masana'antu.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Frafesa Yemi Osinbajo, ya gana da masu ruwa da tsaki kan lamuran kanana da matsakaitan masana’antu a Kano, karkashin shirin gwamnatin tarayya na bunkasa harkokin kasuwanci da samar da rance ga kanana da matsakaitan masana’antu.

Shirin na gwamnati na da manufar samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa ta hanyar raya kananan sana’o’I da masana’antun sarrafa abubuwan bukata domin habaka tattalin arzikin Najeriya.

A yayin ganawar, masu kananan masana’antun sun yi musayar fasaha da mataimakin shugaban na Najeriya ya kan yadda suke muradin gwamnati ta tallafawa harkokin su domin cimma nasara.

Matasa mata da kuma kungiyoyin masu sana’o'I daban daban kimanin dubu talatin ne ake sa ranzasu ci gajiyar samun jari karkashin shirin na gwamnatin Najeriya da mataimakin shugaban kasar ya kaddamar.

Manufar shirin ita ce magance matsalar rashin aiki a tsakanin al’uma da kuma karfafa gwiwar ‘yan kasa su kasance masu dogaro da kansu.

Daga bisani mataimakin shugaban na Najeriya ya kaddamar da shirin gwamnatin jihar Kano na tallafawa matuka baburan Adaidaita sahu da kuma masu sana’ar likin taya domin inganta sanar’ar su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG