Abubuwa na Kara Dagulewa a Mubi Bayan Harin Boko Haram

Boko Haram ta kai a Gwoza, 24 ga Agusta, 2014. (File Photo)

Mazauna garin Mubi arewa-maso-gabashin Nigeria na bayyana fargaba da alhini kan halin da suka shiga bayanda Boko Haram suka abkawa garin.

Mutanen dake zaune a garin Mubi a jihar Adamawa ta arewa-maso-gabashin Nigeria sun bayyana cewa suna fuskantar matsanacin halin kaka-ni-ka-yi a sanadin abkawar da mayakan ‘yan Boko Haram suka yi a cikin garin nasu inda suka hallaka mutane da yawa, suka kori sojoji, suka nakkasa barikin soja kuma suka kokkona wurare da yawa. Wakilin VOA dake Yola, Ibrahim Abdul’aziz ya ce mutanen Mubi na daukar kamar ba gwamnati ne a Nigeria:

Your browser doesn’t support HTML5

Abubuwa na Kara Dagulewa a Mubi Bayan Harin Boko Haram - 3'35"