Wani matashi Ba'amurke da ya shiga gasar Olympic karon farko ya sami zinari
WASHINGTON, DC —
Wani matashi ya samarwa Amurka lambar yabo ta farko a gasar Opympic da ake gudanarwa a PyeongChang, inda ya sami zinari.
Matashin dan shekaru goma sha bakwai Red Gerard, daga Silverthorne, jihar Colorado, wanda karon farko ke nan yake zuwa wasan Olympic, ya sami zinarin ne a gasar wasan tseren kan dusar kankara ta maza.
Gerard ya doke abokan fafatawarsa 'yan kasar Canada ne a karon karshe Max Parrot wanda ya sami azurfa, da kuma Mark McMorris wanda ya sami tagulla karo na biyu bayan gasar Sochi shekaru hudu da suka shige.