An Kaiwai Wasu Sarakuna Farmaki

Marigayi sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta da 'Yan Boko Haram suka kashe.

‘Yan Boko Haram sun kashe sarkin Gwoza.
‘Yan Boko Haram sun kai wani farmaki kan ayarin wasu sarakuna a tsakanin garuruwan Zur, da shaffa ciki

n jihar Borno akan hanyarsu ta zuwa wajen janaizar Sarkin Gombe Alhaji Shehu Abubakar.

Kamar yanda rahotani ke nunawa ‘yan bindigan wadanda sun fi dari sunyi kwanton bauna ne akan hanyar Zur da Shaffa, a jihar Borno.

Inda nan take suka budewa motocin sarakuna wuta da bindigogi, sarakuna da abun ya ritsa dasu, sun hada da Sarkin Uba, Ismaila Mamza da kuma sarkin Gwoza Idris Timta.

Wannan farmakin yayi sanadiyar rasuwar sarkin Gwoza Idris Timta, shidai Sarkin na Gwoza ana haifar ne a shekaran 1948, ya kuma samu ilimisa a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Your browser doesn’t support HTML5

Farmaki Akan Wasu Sarakuna - 1'42"