APC Na Kan Gaba A Jihohin Kudu Maso Yamma

  • Ibrahim Garba

Wani babban allon kampe din APC a Lagos

Yayin da sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun dattawa da na wakilai ke kara fitowa a hukumance, jam'iyyar APC na dada galaba a yankin kudu maso yammacin Najeriya

Rahotanni daga jihohin kudu maso yammacin Najeriya na nuna cewa dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta APC janar Muhammadu Buhari (murabus) ya sha gaban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai mulki Shugaba Goodluck Jonathan. Wakilnmu na Ikko, Babangida Jibrin ya ruwaito babban jami’in bayyana sakamakon zabe na jihar Ogun bayyana sakamakon.

Mr. Babajide Benson na jam’iyyar APC shi ne ya ci zaben Majalisar Wakilai a mazabar Ikorodu na jihar Lagos, kuma bayan zaben ya bayyana ma wakilinmu cewa, zai yi kokarin cika alkawarin tabbatar da cigaban mazabar ta Ikoridu kuma ya na mai kiran da a bashi goyon baya.

Hakazalika, Babangida ya zanta da wasu ‘yan Najeriya game da yadda su ka ga sakamakon zaben ya zuwa yanzu. Mutum na farko y ace bayanai daga jihohin Yarbawa na nuna cewa lallai sun bayar da hadin kai. Don haka y ace ga dukkan alamu babu wata fargaba. To saidai wakiln namu y ace har yanzu ana jiran a kammala hada sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Lagos, bayan tuni aka fara bayyana na wasu jihohin.

Your browser doesn’t support HTML5

SAKAMAKON ZABE A LAGOS 2'10"