Batare Da Bata Lokaci Ba Za a Sake Gina Garin: Hassan Rouhani

Biyo bayan girgizar kasar da ya hallaka mutane da dama da kuma jikkata wasu gwamnatin kasar Iran ta ayyana yau a zaman ranar makoki a kasar.

A yau talata, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya dauki alkawarin cewar gwamnatin sa ba tareda wani bata lokaci ba, zata sake gine wuraren da mummunar girgizar-kasa ta shafa, a yayin da kasar ta ayyana yau a zaman ranar makoki.

Rouhani yayi magana ne a lokacin da ya kai ziyara yankin Kermanshah inda bala’in yafi yin barna a girgizar mai karfin awo 7.3, a ma’aunin mutsin kasa daya afkawa yankin ranar Lahadi, akan iyakar Iran da Iraqi.

kafar yada labaran kasar Iran ta sanar da cewa a kalla mutane 530 ne suka rasa rayukan su kuma mutane 7000 suka ji rauni.

Mafi yawancin wadanda abin ya shafa mazauna Sarpol-e-Zahab ne dake lardin Kermanshah. Sai dai makwabciyarta Iraqi kuma, ma'aikatar cikin gidan kasar ta bayyana cewa mutane bakwai ne suka rasu kuma 500 suka jikkata.