DOMIN IYALI: Bibiya Kan Cin Zarafin Iyali-Kashi Na Daya

Alheri Grace Abdu

Biyo bayan yawan cin zarafin kananan yara da iyaye ke yi, da ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriya, shirin Domin Iyali ya gayyaci wadansu fitattun 'yan fafatukar kare hakkokin mata a Najeriya domin neman hanyar shawo kan wannan mummubar dabi'a.

Shirin ya karbi bakuncin Hajiya Saudatu Shehu Mahdi babbar sakatariyar kungiyar kare hakkokin mata da aka fi sani da WRAPA, da kuma Madam Helen Bako shugabar kungiyar yaki da tashin hankali-Nigerian Women Against Violence, kuma kwararra a fannin kula da jin dadi da walwalar al'umma.

Hajiya Saudatu ta fara yin tsokaci a kan batun nan da muka shafe makonni hudu muna gabatarwa da ya shafi bata wadansu kananan yara a garin Kaduna da ake zargin mahaifinsu da aikatawa.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Tattaunawa kan kuntatawa mata-PT1-10:00"